W.Yah 13:12 - Littafi Mai Tsarki12 Tana zartar da duk ikon dabbar nan ta farko, a kan idonta, tana kuma sa duniya da duk mazauna a cikinta, su yi wa dabbar nan ta farko sujada, wadda aka warkar mata da rauninta mai kamar na ajali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.