Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.
Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.
Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.
Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.