Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.
Domin a rubuce yake cewa, “ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa, Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda, Don yasasshiya ta fi mai miji yawan 'ya'ya.”
Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.
Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa. Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna. Yanzu za ki ƙara samun 'ya'ya fiye da na Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!