Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 12:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar 'yan'uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 12:10
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.


Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.


Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”


Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?


Duk wanda ya ci nasara, yake kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi zan bai wa iko a kan al'ummai,


amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce, “ ‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki, Mulkinka yă zo,


Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”


Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.


Ubangiji Sarki ne, Yana mulki a kan al'ummai.


Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”


Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,


Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu,


Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin! Kana mulkin mallakarka da adalci.


suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”


Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ