W.Yah 11:19 - Littafi Mai Tsarki19 Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.