W.Yah 11:15 - Littafi Mai Tsarki15 Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.