Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”
Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.