Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 11:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Sai suka ji wata murya mai ƙara daga sama tana ce musu, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi sama a cikin gajimare, maƙiyansu suna gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 11:12
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”


Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.


Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.


sa'an nan sai mu da muka wanzu, muke a raye, za a ɗauke mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji.


Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al'ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.


Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.


Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa.


Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai, Kamar kurciyoyi suna komowa gida.


Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.


Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”


Sa'ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal.


Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”


Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.


Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.


Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji, Sa'an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya, Sa'ad da suka ga ka ta'azantar da ni, Ka kuma taimake ni.


Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji? Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?


Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka? Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?


Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa.


Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ