Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 10:6 - Littafi Mai Tsarki

6 ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 10:6
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko, Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa, Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”


Mala'ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”


Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,


Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,


Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ”


Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.


ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.


Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.


sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,


Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.


Saboda haka, sai ku yi farin ciki, ya ku sammai, da ku mazauna a ciki. Amma kaitonku, ke ƙasa, da kai teku, don Ibilis ya sauko gare ku da matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.”


Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ