Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 10:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala'ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 10:10
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.


Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.


Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi, Har sun fi zuma zaƙi!


Da ma ya ji daɗin waƙata, Saboda yakan sa ni in yi murna.


Abin da ake so ne fiye da zinariya, I, fiye da tatacciyar zinariya ma, Sun fi zuma zaƙi, I, fiye da tatacciyar zuma ma.


Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.


Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.


Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”


Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama'a iri iri, da al'ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ