Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 10:1
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.


Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.


Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika, yana shela da murya mai ƙarfi cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?”


Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.


Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.


Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”


Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama. Gajimare ne karusanka, A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.


Gajimare da duhu sun kewaye shi. A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.


Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.


da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.


A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.


“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


Ka kuma rufe kanka da gajimare Don kada addu'a ta kai wurinka.


“Na yi alkawari a zamanin Nuhu, Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba. Yanzu kuwa ina miki alkawari, Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba, Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.


Wannan shi ne jawabi a kan Masar. Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai.


Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta, Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya. Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne, Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.


Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.


Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.


Bayan haka, na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa.


Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce, “Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, yana a riƙe da mabuɗin mahallaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ