W.Yah 1:9 - Littafi Mai Tsarki9 Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.