Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 1:1
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”


Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala'ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”


domin ba daga wurin mutum na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta wurin bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice.


To, ka rubuta abubuwan da ka gani, da abubuwan da suke a nan a yanzu, da abubuwan da suke shirin aukuwa bayan wannan.


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa.


Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice.


Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.


Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”


Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi.


Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”


Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.


Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal.


Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.


Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,


Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wanda yake a zaune a kan kursiyin.


Sai ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwar nan, wadda take zaune a bisa ruwa mai yawa,


Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”


Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.


Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”


Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,


Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.


Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ