har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.
Ku yi murna tare da Urushalima Ku yi farin ciki tare da ita, Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan! Ku yi murna tare da ita yanzu, Dukanku da kuka yi makoki dominta!
Gumakansu dodon gona suke, a cikin gonar kabewa, Ba su iya yin magana, Ɗaukarsu ake yi domin ba su iya tafiya! Kada ku ji tsoronsu. Gama ba su da ikon aikata mugunta ko alheri.”