Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon, Taho daga Lebanon. Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana, Da Dutsen Senir da Harmon, Inda zakuna da damisoshi suke zaune.
Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!
Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi, Mu ga ko sun fara tohowa, Ko furanni sun fara buɗewa. Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure. A can zan bayyana maka ƙaunata.