Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 6:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima, Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza, Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 6:4
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir? Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana, Ko na wata mai kashe ido.


Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo, Mai kyan gani ne na Allah, Birnin babban Sarki. Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!


Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.


Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.


Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini. Suna yi wa Urushalima tsāki, Suna kaɗa mata kai, suna cewa, “Ai, Urushalima ke nan, Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali, Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”


Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata, Ba wanda zai kushe ki!


Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi. Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki, Gama muryarki tana da daɗin ji, Fuskarki kuma tana da kyan gani.


Allah yana haskakawa daga Sihiyona, Da cikar jamalin Sihiyona.


domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.


Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.


A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.


Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.


Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata, Idonki suna haskaka da ƙauna.


Rana ta sa na zama akawala kyakkyawa. Matan Urushalima, bisa ga launi, ni ƙasa ƙasa ce, Kamar alfarwar hamada, Kamar labulen fādar Sulemanu.


A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba'asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.


Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.


Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa, A kagarar birnin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ