Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 6:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir? Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana, Ko na wata mai kashe ido.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 6:10
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima, Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza, Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.


Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta.


Idan ga hasken rana nake zuba ido, Ko ga hasken farin wata ne,


Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.


Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.


domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.


Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.


“Sa'an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, za ku warke nan da nan. Adalcinku zai yi muku jagora, zatina zai rufa muku baya.


Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji, Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?


Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir, Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’


“Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”


Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.


Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.


Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”


Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.


Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu, Na karkashe su da maganar bakina. Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.


Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.


Wace ce take zuwa daga cikin jeji, Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta? A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, A wurin da aka haife ki, Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.


Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.


Amma za su razana, Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.


Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana. Kwanakin ranka mafiya duhu Za su yi haske kamar ketowar alfijir.


Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama, daga bakinsa kuma takobi mai kaifi biyu yake fitowa. Fuskarsa tana haske kamar rana a tsaka.


Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata, Idonki suna haskaka da ƙauna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ