Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 5:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 5:2
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.


Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi. Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki, Gama muryarki tana da daɗin ji, Fuskarki kuma tana da kyan gani.


Mala'ikan da yake Magana da ni ya komo ya farkar da ni kamar yadda akan farkar da mutum daga barci.


Amma ɗaya kaɗai nake ƙauna, Ita kyakkyawa ce kamar kurciya. Tilo ce ga mahaifiyarta, 'yar lele ce ga mahaifiyarta. Mata duk sukan dube ta, su yaba. Matan sarki da ƙwaraƙwaransa suka raira waƙa suka yabe ta.


Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu, Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.


Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”


Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum.


Na tsiraita ga masu dūkana. Ban hana su sa'ad da suke zagina ba, Suna tsittsige gemuna, Suna tofa yau a fuskata.


Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba. Ba rigyawar da za ta nutsar da ita. Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya, Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.


Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne. Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena, Ya gangara leɓunan masu barci.


Gashin kansa dogaye ne suna zarya, Baƙi wulik kamar jikin shaya. Kansa ya fi zinariya daraja.


Kallon idonki, budurwata, amaryata, Da duwatsun da suke wuyanki Sun sace zuciyata.


Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata, Ba wanda zai kushe ki!


Ina kwance a gadona dukan dare, Ina mafarki da ƙaunataccena, Na neme shi, amma ban same shi ba. Na kira shi, amma ba amsa.


Ƙaunataccena ya yi magana da ni. Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.


Na ji muryar ƙaunataccena! Ya zo a guje daga kan tuddai, Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.


Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali.


Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.


Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.


Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,


Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta.


Saboda haka aka ce, “Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu. Almasihu kuwa zai haskaka ka.”


An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.


Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa.


Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]


Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.


A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah.


Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can.


Sa'ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye.


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa. Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.


Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi! Na so in ji muryarsa ƙwarai! Na neme shi, amma ban same shi ba. Na yi kiransa, amma ba amsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ