Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.
“Haka Allah zai sa wa zuriyata albarka, Gama ya yi mini madawwamin alkawari, Duka kuwa a shirye yake, zai kuwa kiyaye. Abin da nake bukata ke nan, Wannan ne nasarata, Na tabbata kuwa Allah zai kammala shi.
An dalaye ginshiƙanta da azurfa, An rufe ta da zane da aka yi wa ado da zinariya. An lulluɓe wurin zama da zanen shunayya. Matan Urushalima sun yi mata irin yayin da ake yi na ƙauna.