Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!
Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.
Kwana guda da za a yi a Haikalinka, Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam. Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna, Da in zauna a gidajen mugaye.
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara, Mu yi bikin cin nasara da ka yi, Da yabon Ubangiji Allahnmu. Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!
Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata, Ina tattara mur da ƙaro. Ina shan zuma da kakinsa. Ina shan ruwan inabi da madara kuma. Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!
Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.
Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.