Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man.
Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.
An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa ulun, ta tsiyaye masa man a kā.
Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.
Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’