Titus 3:7 - Littafi Mai Tsarki7 Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.