“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.
“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi, In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada. Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku, In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.
Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.
Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”
Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.