Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Titus 3:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin shari'a, da Afolos, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Titus 3:13
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske.


Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce,


Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.


Kada fa kowa yă raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da 'yan'uwa.


ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku.


Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.


Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?”


Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”


Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”


Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?”


Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.


To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al'ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan 'yan'uwa ƙwarai.


To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,


Ga zancen ɗan'uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don yă zo wurinku, tare da saurar 'yan'uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa'ad da ya ga ya dace.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ