Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al'amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.
Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa'adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,