Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.
To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,
Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai.
Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.
A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne! Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta, Ba za a iya kaushe ta ba, Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”
wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.
Da jama'a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.
‘Mene ne kai, ya babban dutse? Za ka zama fili a gaban Zarubabel, zai kuwa kwaso duwatsun da suke ƙwanƙoli da sowa, yana cewa alheri, alheri ne ya kawo haka.’ ”
Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.