mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.
Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.
Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!