Rut 4:17 - Littafi Mai Tsarki17 Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa'an nan Yesse ya haifi Dawuda.