Rut 2:20 - Littafi Mai Tsarki20 Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”