Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Rut 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Rut 1:6
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace, Zan ƙosar da matalautanta da abinci.


Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci, Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.


Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.


Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.


su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”


“Ubangiji Allahn Isra'ila, A gare shi ne lalle yabo yake tabbata, Domin ya kula, ya yi wa jama'a tasa fansa.


“Ubangiji ya ce, ‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.


“Maganata kamar dusar ƙanƙara take, Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba, Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.


Gaɓar teku za ta zama ta mutanen Yahuza waɗanda suka ragu, Wurin da za su yi kiwo. Za su kwanta da maraice a gidajen Ashkelon, Gama Ubangiji Allahnsu zai kula da su, Zai kuwa mayar musu da albarkarsu ta dā.


A yanke shari'arsa yakan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan kuɓutar da ɗaurarru.


Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,


Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi 'ya'ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama'ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.


Sa'an nan Yusufu ya rantse wa 'ya'yan Isra'ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.”


Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka.


Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa,


Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta.


Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.


To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.


Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya, Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.


Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata,


sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.


Bayinka suna ƙaunarta, Ko da yake an hallakar da ita, Suna jin tausayinta, Ko da yake ta zama kufai.


Sa'an nan ya ce musu, “Ga shi, zan ba ku hatsi da ruwan inabi, da mai, Za ku ƙoshi. Ba zan sa ku ƙara zama abin zargi ga al'ummai ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ