Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.
Ubangiji ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku, Ku da kuka zo gare ni neman taimako. Ku yi tunanin dutse inda kuka fito, Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.