Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 9:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 9:18
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.


“Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.


Don me ka bari muka ɓata daga al'amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.


Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


Amma zan taurare zuciyar Fir'auna don in aikata alamu da mu'ujizai cikin ƙasar Masar.


Ubangiji kuma ya taurare zuciyar Fir'auna har ya ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa wa Musa.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu'ujizai nawa a tsakiyarsu,


Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.


Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna har bai yarda ya sake su ba.


Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.


Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.


Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.


“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”


'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.


Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ