Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.
domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.
yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.
Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,
An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.