Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 8:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 8:35
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.


Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce. Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,


Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.


Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.


Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.


In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.


Ubangiji ya bayyana gare ni tun daga nesa cewa, “Ya Isra'ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba. Zan sāke gina ki, Za ki kuwa ginu, Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe, Za ki shiga rawar masu murna.


Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.


To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,


suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


Rabuwata da matsaran ke nan, Sai na yi kaciɓis da ƙaunataccena. Na riƙe shi, ban sake shi ba, Na kai shi gidanmu, har ɗakin mahaifiyata.


Duk waɗanda suke aikata mugunta za su sha wahala da masifa, da fari Yahudawa, sa'an nan kuma al'ummai.


Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.


Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.


Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka, ba a ci ɗunguminmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba.


Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu a ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba.


Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.


ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ