Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 8:3
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari'ar Musa ta kuɓutar da ku.


Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.


Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.


Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.


Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.


Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?


Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.


Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa,


sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.


Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah,


Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.


Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.


Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”


Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun.


Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara.


Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.


Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ