Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 8:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 8:23
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.


Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.


Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.


muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,


Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.


Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa?


Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah.


Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne.


Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.


Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.


ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.


domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.


Ko a lokacin da muka zo ƙasar Makidoniya ma, ba mu sami shaƙatawa ba, ana ta wahalshe mu ta kowace hanya, a waje ga husuma, a zukatanmu kuma ga fargaba.


Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.


Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri,


Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.


Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ