A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa'ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.
Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.
Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.
Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba.
“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.
Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.