Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.
Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!
Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.
Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.
a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.
Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.
Na san wani mutum wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka ɗauke shi zuwa Sama ta uku bisa ga ikon Almasihu, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani.
Baiwar nan kuwa dabam take ƙwarai da hakkokin zunubin mutum ɗayan nan. Don kuwa hukuncin da aka yi a kan laifin mutum ɗayan nan, shi ya jawo hukuncin hallaka. Amma baiwar nan da aka yi a sanadin laifofi da yawa, ita take sa kuɓuta ga Allah.
Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.
In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.