Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ai, dā sa'ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha'awa wadda faɗakarwar Shari'a take sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 7:5
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.


Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.


Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”


Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.


To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.


Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.


Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.


Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari'a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi.


Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha'awace-sha'awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba?


Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.


Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.


Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).


Amma ina ganin wata ka'ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka'idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa'idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina.


Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.


Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.


Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.


don Shari'a tana jawo fushin Allah. A inda ba Shari'a kuwa, ba keta umarni ke nan.


Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.


Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram.


Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.


Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.


Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ