Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.
“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,
sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali,
Ya ce masa, “Ka ratsa cikin birni, wato Urushalima, ka sa shaida a goshin mutanen da suke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin.”
An yashe ni a cikin matattu, Kamar waɗanda aka karkashe, Suna kuma kwance cikin kaburburansu, Waɗanda ka manta da su ɗungum, Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.
Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.