Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.
Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.