Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 6:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Mun sani tun da yake an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 6:9
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.


ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.


Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.


Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.


wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa.


Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.


Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ