Romawa 6:21 - Littafi Mai Tsarki21 To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.