Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.
Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.