Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.
Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana.