Romawa 5:17 - Littafi Mai Tsarki17 In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.