Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
Kai wane ne har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya, ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya.