Romawa 3:5 - Littafi Mai Tsarki5 In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.