Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 3:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 3:25
51 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.


Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.


To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.


Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,


domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.


Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu, “Ubangiji ya ceci jama'arsa!”


Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.


To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.


Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,


Mutane masu irin wannan magana, ai, sun bayyana a fili, suna neman wata ƙasa ta kansu ne.


Adalcinka zai tabbata har abada, Dokarka gaskiya ce koyaushe.


In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.


Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa'ad da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya, wato shi da ya yi na'am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,


A bisa akwatin alkawari kuma akwai kerubobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa murfin akwatin nan laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla filla ba a yanzu.


Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.


Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.


domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.


Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?


Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.


Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.


Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.


Sammai suna shelar adalcinsa, Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.


Sammai suna shelar adalcin Allah, Domin shi yake yin shari'a!


Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba, Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe. Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka, Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.


Amma a wanda kuri'ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.


Ubangiji ya bayyana cin nasararsa, Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma.


Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al'ummai su yi yadda suka ga dama.


To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai.


Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,


Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.


shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ