Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 3:19 - Littafi Mai Tsarki

19 To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 3:19
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”


To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su.


domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.


Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam yă yi fariya a gaban Allah ne.


gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.


Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna, Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.


Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?


domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah.


Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari.


Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.


Yakan sa matalauta su sa zuciya, Ya sa mugaye su yi shiru.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa, “Don maganarka tă tabbatar da adalcinka, Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”


Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah.


An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.”


Sarki zai yi farin ciki ga Allah, Duk waɗanda suka yi alkawarai da sunan Allah Za su yi murna, Amma za a rufe bakunan maƙaryata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ